zamu kasance abin dogaron ku wajen samar da labarai na gaskiya, nishadi da tabbatar da hakkin dan Adam

Game da Mu

Zamani Riga!  Zamani Riga!!  Zamani Riga!!!

*Siyasa   *Kimiyya da Fasaha   *Addini

*Tattalin Arziki  *Harkokin Lafiya   *Ci gaban mata

*Zamantakewa  da Al’adu   *Nishadantarwa

 Salo:  Labarai, Rahotanni, duk cikin sauti da rubutu da kuma bidiyo

 Kafofi: Facebook, Twitter & Instagram

Saurare da bibiyar tsarabobinmu na siyasa  a shafukanmu na social media za su sababba sanin makama da kwarewa ga ‘yan siyasa da masu sha’awar al’amuran siyasa musamman matasa.

‘Waina da ruwa’  zai ke kawo muku yadda ake toya waina da ruwa a Amurka da sauran qasashen duniya. Za mu ke lekawa fadin duniya birni da kauye mu gano gudunmawar mata da ci gabansu a kowane fanni.

Kasuwanci da noma a zamanance, wasannin gargajiya da na zamani don karuwa da samun nishadi. Abubuwan ta’ajibi da fahimtar juna kuwa a harkar zamantakewa za a same su kunshe cikin ‘Allah daya..

Waiwaye

Tunanin Zamani Riga na yanzu ya samo asali ne daga Shirin rediyo a Rediyo Kanon Najeriya, wadda shiri ne na siyasa wadda ya rika sharhanta sabatta-juyatar siyasa a jihar Kanon har ma kuma da tsokaci akan siyasar sauran sassan Najeriya. Shirin da kwararren ma’aikacin rediyon nan Umar Muhammad ya rika tsarawa da gabatarwa tare da mataimakansa Sule B. K Zaria da Shazali Adamu.

Zamani Riga na yanzu ya na kan internet bisa adireshin zamaniriga.news domin kewaya duniya baki daya; daga wannan nahiya zuwa waccan:  Amurka, Turai, Asiya balle kuma Afrikarmu

Zamani Rigan Rediyo Kano a jumhuriyar Najeriya ta biyu ya shahara da saka muryoyi dauke da ra’ayoyi da akidun siyasa na hakika na gaskiya na kishin kasa na gwarzayen ‘yan siyasa mazan jiya da suka yi suhuru a wancan zamani  irin su marigayi Mallam Aminu kano, shugaban Jam’iyyar PRP na kasa baki daya, da Albert Ikoku sakataren Jam’iyyar ,Dr. Salihi Iliyasu Shugaban Jamiyar PRP na tsohuwar Jihar Kano, da marigayi gwamnanr Jihar kano, Alhaji Muhammad Abubakar Rimi (Limamin Chanji), na Jam’iyyar PRP da marigayi gwamnar Jihar Kaduna Alhaji Balarabe Musa, Jam’iyyar PRP da marigayi Gwamnar Jihar tsohuwar Gongola ,Alhaji Muhammad Barde, Jam’iyyar GNPP, da marigayi tsohon gwamnan jihar Borno Alhaji Muhammadu Gwani Jam’iyyar GNPP, da tsohon Gwamnan jihar Plateau Solomon Lar, Jam’iyyar NPP tsohon gwamnan Jihar Anambra, Jim Owobodo Jami’iyyar NPP da tsohon gwamnan jihar Imo Samuel Onunaka Mbakwe, Jam’iyyar NPP, tsohon gwamnar jihar Oyo Chief Bola ige, Jam’iyyar UPN da tsohon gwamnan jihar Ogun, Olabisi Onabanjo, Jam’iyyar UPN, da tsohon gwamnan Jihar Lagos Lateef Jakande, Jam’iyyar UPN, tsohon Gwamnan Jihar Ondo Michael Adekunle Ajasin Jam’iyyar UPN da tsohon gwamnan jihar Bendel Ambrose Alli na Jam’iyyar UPN.

Sai dai kash! bayan siyasar ta dauko armashi saboda fafatawa  tsakanin masu ra’ayin kawo sauyi da kuma masu son a dawwama a tsarin zalunci, sai kwatsam a shekarar 1983  soja suka shigo suka hambarar da gwamnatin farar hula a karkahin jagorancin Muhammad Buhari.

Tarihi kan maimaita kansa ko kwana kusa ko bayan lokaci mai tsawo.  A shekarar 2021 da kuma shekarar 2023 an samu wasu ‘yan juyin juya hali wadanda suka nemi su kifar da gwamnatin Amurka lokacin da suka kai hari a babbar majalisar qasar dake babban birnin tarayyar qasar a Washington DC da kuma  makamancin irin wannan tarzoma da akayi a majalisar  qasar Brazil wadda aka nemi a kifar da gwamnatin ta Brazil.

To me ya hada wannan labarin kuma da zamani riga? Abin da nake so a fahimta abin da ya faru a wadannan manyan qasashe Kano ta fara aiwatar da irin wannan tarzoma kafin wadannan qasashe su gani suyi koyi. An kone kadarorin gwamnati a waccan lokaci domin kawai a kada gwamnatin da mafiya rinjayen talakawa suka zaba.

Kuma babban wani abin takaici, da jimamin talakawa shi ne kisan gilla da aka yiwa marigariyi dan kishin qasa Dr. Bala Muhammad. Allah ya jikansa ya ba shi gidan Aljanah.

Kamar yaya? Kin tuna Hausawa sun ce sai an buga akan san na qwarai. A wancan lokacin tsohuwar gwamnatin jihar kano da al’ummar jihar kano sun taka rawar siyasar da ta karade jihohin arewacin Nigeria, Siyasa mai tsafta, Siyasa mai albarka, Siyasa ta gaskiya, siyasar akida da tsantsar talakawa ba za su manta da ita ba.

Kwarai kuwa, talakawa ba za su manta da gwamnatocin ceton talakawa da aka yi musamman a tsofaffin jihohin Kano da Kaduna ba. A matakin farko sun sami ‘yancin su fada a saurare su domin kuwa mafi yawan wakilansu a majalisun dokoki da sauran sabgogin gwamnati daga cikinsu suka fito. An ba da kulawa sosai wajen raya yankunan karkara wajen sama musu hanyoyin mota da ruwan famfo da wutar lantarki da bunkasa noma ta hanyar wadata manoma da takin zamani da magungunan feshin kashe kwari masu lalata amfanin gona da dai sauransu. Dauki misalin jihar Kano, gwamnatin limamin canji Muhammadu Abubakar Rimi ma’aikata ta kafa sukutum ta raya karkara baya ga soke haraji da jangali da tayi. Ga hukumar samar da wutar lantarki a yankunan karkara da kamfanin samar da kayayyakin bunkasa noma na KASCO. Ilimi da harkar lafiya sun sami tagomashi inda aka gina matsaikatan asibitoci a hedkwatocin kananan hukumomi. Haka kuma gwamnatin Limamin canji ta PRP ta ciyo lambar hukumar UNESCO ta majalisar dinkin duniya kasancewarta gwamnati mafi himma a nahiyar Afrika wajen yaki da jahilci. Ta ciyo.

Shin juyin mulkin soja da juyin juya halin tarzomar kifar da gwamnati yanzu sun zama tsohon yayi anan Nigeria ko a  duniya ko a’a? Lokaci ne zai tabbatar da haka.